1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Najeriya: Komawa ga noma da ma'adinai

October 4, 2023

A wani mataki na kauce wa dogaro da hajar man fetur, masu ruwa da tsaki a harkokin noma da ma'adinai a Tarayyar Najeriya na can na nazarin hanyoyin habaka fitar da albarkatun kasar zuwa waje.

Najeriya | Noma | Ma'adinai | Mafita | Kudin Shiga | Man fetur
Najeriyar dai, ta yi fice a harkar noman shinkafaHoto: Imago Images/photothek/T. Imo

Masu ruwa da tsaki da harkokin noma da ma'adinan na Tarayyar Najeriya dai, sun dauki wannan matakin ne da nufin samun kudin shiga da kasar ke cikin  bukatu yanzu. Man fetur ne dai ya dau Najeriyar zuwa wani matsayi tun daga shekarun 1970, kuma daga dukkan alamu masu mulkin kasar na neman kaucewa hajar da ke dada nuna alamun gaza daukar bukatun 'yan mulkin a halin yanzu. Sabuwar dabarar Najeiryar dai na zaman noma da ma'adinai, cikin neman sauki da kara samun kudin shiga na dalolin da kasar ke ta karanci yanzu. Wani taro na kwarraru da ragowar masu ruwa da tsaki a sarrafa kayan noma da ma'adinai dai, ya share tsawon wuni guda yana tunanin mafita ga kasar da ke da dimbin albarkatun kayan noma amma kuma ke karewa a cikin la'ada.

Karin Bayani: Karin farashin man fetur a Najeriya

A bara kadai Najeriyar ta samu abun da ya kai kusan  dalar Amurka miliyan 5000 daga kayan gona da ma'adinan da ta fitar zuwa waje, adadin kuma da Abujar ke fatan kara yawansa da kila ma zarce wa man fetur din da ke zaman hanyar samar da kudi irin ta gadon gado. Ko bayan man kadanya dai, suma masu noma da sarrafa bi-rana ko kuma itaciyar Sun flower a Najeriyar, sun ce kasar tana shirin samun riba babba a nan gaba a fadar Jibrin Bukar da ke zaman shugaban kungiyar manoma da masu sarrafa bi-rana a Najeriyar. To sai dai kuma in har masu noma da sarrafa kayan gonar suna ta tsallen murnar hango dama, babban kalubale cikin harkar noma da sarrafa kayan dai na zaman rashin kudi da tsadar bashi na bankuna. Mafi yawan bankunan Najeiryar dai na da kudin ruwan da ya kai kusan kaso 28 cikin 100, adadin kuma da ya wuce da tunanin masu sana'ar noma da sarrafa kayanta.

Matsalolin tsaro na tarnaki ga manoma

04:14

This browser does not support the video element.

Yahaya Jibrin Harbau dai na zaman jami'in inganta fitar da kaya zuwa waje na bankin FCMB da ke kula dasashen arewacin Najeriyar, kuma ya ce bankunan suna bukatar sassauta tsarin hulda da masu fitar da kayan zuwa waje da nufin taimaka wa kananan 'yan kasuwar cikin kasar. Kimanin kayan noma da ma'adinai 167 ne dai Najeriya ke hada-hadarsu a ciki da ma wajen kasar, kuma tuni Abujar ta sanar da matakan saukaka fitar da kaya zuwa waje ko bayan sassaucin haraji da ma garabasa ga kamfanoni da ke sana'ar mai tasiri. Kuma ko bayan ita kanta tarayyar, suma jihohin kasar na laluben hanyoyi na taimaka wa sano'in da ke cikin jihohin nasu. Salisu Shehu dai na zaman babban sakatare a ma'aikatar ciniki da kasuwanci a jihar Sakkwato, kuma ya ce fitar da albasa da tarfanuwa na iya rike jihar ko ba man fetur in har aka iya kyautata harkar noma da sarrafa su.

Karin Bayani: Horas da mata alkinta kayan lambu

Babban kalubale ga Najeriyr a halin yanzun dai, na zaman samun masu zuba jari na sarrafa kayan noman da ma'adinai cikin kasar da nufin iya samun karin kudin shiga da ma aikin yi. Mafi yawan kamfanonin waje dai na zabar kwasar danyun kayan da kamfanonin ke bukata tare da kai su wajen Najeriyar a sarrafa su, abun kuma da acewar Abdullahi Sidi Ali da ke zaman tsohon darakta a Hukumar Habaka Fitar da Kaya Kasashen Waje ke zaman gada a tsakanin kasar da kai wa ya zuwa ga bukatun rayuwa. Abun jira a gani dai, na zaman yadda take shirin kaya wa a tsakanin Najeiryar da ke tunanin dama a cikin harkar noman da kila ma'adinan da masu jari na wajen da ke ta jan kafar zuba jari cikin rashin tsaro.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani