1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Komawa karatu a Chadi da Ghana

Inshola Yussif Abdul Ganiyu GAT | Abdoulrazak Garba Babani GAT
June 25, 2020

An koma karatu a kasashen Ghana da Chadi a wannan Alhamis bayan hutun cilas na annobar Corona. Sai dai a duk kasashen biyu komawa makarantar ta zo da matsaloli da ke da nasaba da rashin kayan kariya a makarantun.

Liberia leeres Klassenzimmer einer Schule in Monrovia
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo


A kasar Chadi a wannan Alhamis ce 25/07/2020 aka koma karatu a makarantun bokon kasar bayan hutun cilas na tsawon watanni uku da aka dauka a sakamakon annobar Coronavirus.

Shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby Itno ne dai da kansa ya bukaci da a koma makarantar domin tsira da karatun wannan shekara a fadin kasar. To sai dai kungiyar malaman makarantun boko ta kasar wato SET ta gindaya wasu sharudda wadanda ta ce idan dai gwamnatin ba ta cika su ba to komawa makarantar zai kasance suna kawai. Daga cikin jerin bukatun da kungiyar malaman makarantun bokon kasar ta bukaci gwamnati ta cika sun hada da samar da takunkumin kariya da sinadarin wakin hannu ga malamai da dalibai a illahirin makarantun bokon kasar. 

Hoto: DW/L. da Conceição

Kazalika kungiyar malaman makarantun bokon kasar ta Chadi wato SET ta bukaci a takaice yawan dalibai a ajujuwan jarabawa zuwa dalibai 25 ko 30 a maimakon 100 zuwa 120 da ake samu a wasu ajujuwan, wannan kuwa domin samun sukunin ci gaba da bai wa daliban darussa ba tare da hadarin kamuwa da cutar ta Covid-19 ba.

Wani kalubalan na daban da ke tattare da shirin komawa makarantar shi ne saukar damina a wasu yankunan kudancin kasar ta Chadi inda ajujuwa da dama suka kasance na zana. Bugu da kari dalibai da dama sun koma a kauyikansu domin taya iyayensu aikin gona inda a halin yanzu kuma suke fuskantar matsalar rashin samun motocin sufuri da za su yi jigilarsu zuwa wuraren jarabawar, baya ga kangin talauci da ya yi wa iyayen daliban katutuwa.

Hoto: DW/B. Ndomba

A kasar Ghana ma a wannan rana ce aka koma makarantar bayan dawowa daga hutun cilas na Corona. Sai dai a can ma duk kanwar ja ce inda ake fuskantar matsaloli dabam-dabam na tafiyar da karatun. Da farko dai iyaye da dama ne ke dari-dari wajen turo da yaran nasu makaranta a bisa fargabar kamuwa da cutar da Covid 19 wacce har yanzu ke ci gaba da yaduwa a kasar. A hannu guda kuma gwamnatin kasar ba ta tanadi matakan kariya ga malamai da dalibai a makarantun kasar ba a wannan rana. Lamarain da ya sanya komawar ta yau ta kasance kusan suna a makarantun bokon kasar da dama.