Komawar zirga zirgar jiragen sama a Spain
December 4, 2010Kusan ɗaukacin ma'aikatan kula da sauka da tashin jiragen sama a ƙasar Spain sun koma bakin aikin su bayan yajin aikin da suka shiga a wannan Asabar, kana jim kaɗan bayan da gwamnati ta ayyana dokar ta ɓaci da kuma yin barazanar ɗaukar matakin hukunta su. Yajin aikin da ma'aikatan suka shiga akan yawan sa'oin aiki dai ya janyo matsala ga kimanin fasinjoji dubu 300 da ke dawowa daga hutun ƙarshen mako, abinda yasa gwamnatin ƙasar ta Spain ta umarci sojoji su kula da filayen jiragen kana ta yi barazanar jefa duk wani ma'aikacin daya ƙauracewa wurin aikin sa a cikin gidan yarin.
A cewar wani kakakin hukumar dake kula da sha'anin tafiyar da filayen jiragen, kusan ɗaukacin ma'aikata 184 da ke kula da harkokin tashi da kuma saukar jiragen sama sun zo wuraren aikin su, wanda ya bada damar fara zirga zirgar jiragen sama a yanzu.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Muhammed Abubakar