Komiotin sulhu ya girka kotun mussamman a kan mutuwar R. Hariri
May 31, 2007Komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin dunia ya kaɗa ƙuri`ar amincewa; da girka kotun mussamman; da zata gudanar da bincike, ta kuma yanke hunkunci, a game da kissan tsofan Praminsitan Libanon Rafik Hariri.
ƙasashe 10, daga jerin ƙasashe 15 membobin komitin sulhu su ka amince da girka wannan kotu.
Ƙasashen 5 da su ka ware, sun haɗa da Russie, Sin,Afrika ta Kudu, Indonesia da Qatar.
A watan februaru na shekara ta 2005, wasu yan takife, su ka hallaka Raffik Hariri, tare da ƙarin mutane 22, a birnin Beyruth.
Ranar 10 ga wannan wata, aka tsara kotun zata fara aiki, to amma har ya zuwa yanzu, babu taƙamemen wuri, da aka keɓe domin girka opisoshin ta, saidai a ana kyautta zaton, ta kasance a ƙasashen Saiprus, Italia, ko kuma Holland.
Jikadan ƙasar Syria a Majalisar Ɗinkin Dunia Bachar Jafari,ya yi matuƙar suka ga wannan kotu , wadda a cewar sa, ba ta wani anfani, ga al´ummar ƙasar Libanon.