1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korafe-korafe dangane da nadin ministocin Tibunu

August 17, 2023

Masu ruwa da tsaki na martani kan ma'aikatu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya raba wa sabbin ministoci bayan share watanni na jira. Fannin tattalin arziki ya koma kudancin Najeriya yayin da aka kyale tsaro a sashen Arewa.

Tinubu ya shafe kwanaki 100 a mulki kafin ya nada ministocinsa
Tinubu ya shafe kwanaki 100 a mulki kafin ya nada ministocinsaHoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Ma'aikatun tattali na arziki ya zuwa ga ma'adinai na karkashin kasa da ruwaye da sadarwa da daukacin harkar man fetur duk suna karkashin moinistoci na kudancin tarrayar Najeriya, a yayin da batun tsaro ya tashi da ministoci har guda biyu duk na Arewa baya ga ministan 'yan sanda da minitan cikin gida da ma masharwacin tsaron kasar. Dr Yahuza Getso da ke zaman kwarrare kantsaron ya ce tsarin gwamnatin Tinubu na zaman babban sako ga sashen arewacin kasar.

Wani tsarin da ya kara fitowa fili daga zabin na Tinubu na zaman yadda aka rika hada manya da kananan ministocin na ma'aikatu guda daga sashen arewacin kasar. Alal misali, daukacin ministocin ilimi sun fito daga Arewa ba ya ga ma'aikatar gida da raya birane. Sannan na tsaron da ministocin albarkatun ruwa  ma sun zama wakilan Arewa.

Nyesom Wike ya zama dan Kudu na biyu da ya zama ministan AbujaHoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

An dauko tsohon gwamnan Rivers Nyesom Wike tare da ba shi ministan Abuja. A karon farko, wani mutumin kudancin kasar zai jagoranci ma'aikatar ta Abuja mai tasiri tun bayan Mabolaji Ajose adegun da ya zamo ministan farko a cikin birnin a lokacin da aka kafa shi. Shugaban a karon farko na lokaci mai nisa ya dauki fararen hula ya kuma mika musu batun tsaron kasar da ke fuskantar karuwar rigingimun rashin tsaron. Saii dai Dr Husaini Tukur Hasan ya ce dabarun  Tinubu ba su saba da tsohuwar al'adar tarrayar Najeriyar ba.

Shugaba Tinubu na neman farfado da darajar Naira da tattalin arzikin NajeriyaHoto: Ubale Musa/DW

Babban fata da buri na zaman iya kaiwa ga sake farfado da tattalin arzikin Najeriya da ke cikin laka, ko bayan  samar da tsaron da ke nuna alamun dada lalacewa a yanzu. Sai dai Senata Umar Tsauri dake zaman jigo a jam'iyyar PDP ta adawa ya ce da kamar wuya a iya tatse ruwa  ga gwamnatin da ke fadin a sake lale.

Bayan jira na kwanaki 100, hankali 'yan Najeriya daga dukkan alamu na shiri karkata zuwa ga shekara ta farko ta gwamnatin Tinubu da ta fara da zunguro sama da kara, kuma ta ce tana da burin sauya rayuwa a lokacin kalilan.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani