Korafi kan hana bakin haure shiga Nijar
December 2, 2016Matakin da gwamnatin Nijar ta dauka na tsaurara bincike a iyakokinta kan batun shige da fice musamman ma a yankunan da lamarin kwararar bakin haure ya yi kamari kamar jihar Agadez na cigaba da haifar da mahawara tsakanin masu rajin kare hakkin bani Adama a kasar. Ibrahim Manzo Diallo na kungiyar farar hula ta ya ce wannan yanayi abu ne marar dadi duba da irin yadda jami'an tsaro kan dauki tsauraran matakai kan duk wanda aka gani dauke da jama'a a cikin motarsa ko da kuwa ba bakin haure ba ne.
Sababbin matakan na tsaurara tsaro a iyakokin shigowa da ficewa daga Nijar din a cewar masu sharhi wani somin tabi ne na dangantakar ta Turai da Nijar don tabbatar da batun na kakkabe bakin haure inji Malam Saidou Abdou wani masanin a fannin shige da ficen jama’a da ke Nijar sai dai kuma wasu na cewar hakan zai yi nakasu ga irin yarjejeniyar da ake da ita ta zirga-zirga tsakanin jama'a da ke kungiyar kasashen ECOWAS ko CEDEAO domin kuwa aki yiwuwar a yi kuskure kame wanda ba bakin haure ba a matsayin wanda ke son tafiya Turai ta hamadar sahara.
Ko da ya ke hukumomin kasar har yanzu sun ki su ce uffan kan sabbin matakan na tsaro amma tun a baya gwamnatin ta Renaissance ta kudri anniyar dakile matsalar ta hanyar kafa wasu hukumomin da za su bata shawarwari game da sababbin dubaru na tsaro ciki kuwa har da hukumar CNESS da ke shirin tallafawa gwamnatin da wasu rahotanni. A baya ma ministan cikin gidan kasar Malam Bazoum Mohamed ya ambato akalla mutun 47 da wasu motoci 63 tare da mayar da wasu dubban bakin haure a cibiyoyin OIM daga tsakiyar saharar kasar.