Korar 'yan gudun hijirar Cote d'Ivoire daga Isra'ila
June 24, 2012A wannan Lahadin (24. 06. 12) wata kotun Isra'ila ta yanke hukuncin amincewa da korar 'yan gudun hijirar ƙasar Cote d'Ivoire dake zaune a ƙasar ba bisa ƙa'idah ba, abinda ya share fagen fitar da wasu 'yan gudun hijirar ƙasar ta Cote d'Ivoire kimanin 2000. A dai shekara ta 2004 ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana Cote d'Ivoire a matsayin ƙasar dake fama da rigingimu rin na yaƙin basasa, amma kuma yaƙi ya ƙare, kana Allasane Ouattara ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar a shekara ta 2011, wanda akan hakane Isra'ila ta ce za ta soke manufar bada kariya ga 'yan gudun hijirar da suka fito daga ƙasar ta Cote d'Ivoire.
Wata kotu a birnin Qudus ta yi watsi da ƙarar da wasu 'yan gudun hijirar Cote d'Ivoire 131 suka shigar a gabanta domin mayar musu da matsayin su na 'yan gudun hijira ko basu damar sake gabatar da buƙatar zama 'yan gudun hijira, ko kuma kyalewa su zauna a cikin Isra'ila domin dalilai na jin ƙai.
A cikin wata sanarwar daya fitar, ministan kula da harkopkin cikin gidan Israila Eli Yisha ya yi marhabin lale da hukuncin kotun, amma ya ƙara da cewar babbar matsala, ita ce ta 'yan gudun hijirar da suka fito daga ƙasashen Eritriya da Sudan, waɗanda ya ce adadin su ya kai dubu 50.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar