Koriya ta Arewa da ta Kudu sun cimma matsaya
August 24, 2015Koriya ta Arewa da ta Kudu sun kammala tattaunawar da suka kaddamar don kawo karshen rikicin da ya kusan tura su cikin wani yanayi na yaki. Bangarorin biyu basu riga sun mayar da martani dangane da sakamakon taron ba, amma kamfanin dillancin labaran Koriya ta Kudu na Yonhab ya ce bangarorin biyu sun cimma matsaya, kuma ma har Koriya Ta Arewa ta yi nadaman irin matakan da ta dauka a baya-bayan nan. Sannan ita kanta Koriya ta Kudu ta ce za ta daina yada labaran Farfagandan da take yi ta lasifika a Koriya ta Arewar. Fadan shugaban kasar Koriya ta Kudu ta sanar cewa wakilinta a taron mai ba da shawara kan tsaro Kim Kwan-Jin sai sanar da sakamakon taron.
Tun da yammacin asabar ne dai bangarorin biyu suka fara wannan tattaunawa domin daidaita tsakaninsu tun bayan da rikici ya fara ta'azara tsakaninsu a watan da ya gabata, sakamakon fashewar wasu nakiyoyi a kan iyakokinsu, wadanda suka yi ajalin dakarun Koriya ta Kudun biyu