1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kim Jong Un da makami mai linzami

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 16, 2018

Kafar yada labaran Koriya ta Arewa ta tabbatar da cewa kasar ta sake yin gwajin sabon makami mai linzami.

Nordkorea Kim Jong Un testet Hightech-Waffe in Pjöngjang
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya jagoranci gwajin sabon makami mai linzamiHoto: Reuters/KCNA

Rahotanni sun nunar da cewa Shugaba Kim Jong Un na kasar ne, ya sanya idanu yayin gwajin makamin. Kamfanin dillancin labaran kasar ya bayyana cewa sabon makamin, zai sake tsaurara tsaro da kuma karfafa sojojin kasar. Shugaba Kim ya bayyana jin dadinsa matuka kan gwajin da ya ce ya cimma bukatunsu.