1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKoriya ta Arewa

Kim Jong Un ya kaddamar da babban taron kasa

Abdourahamane Hassane
December 27, 2023

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya kaddamar da babban taron karshen shekara na jam'iyyar Ma'aikata mai mulki.

Nordkorea | Kim Jong Un
Hoto: KCNA/KNS/AFP

 Wannan taro ya zama dandali na daukar sabbin matakai ga shugaban wanda,a bara a irin wannan taro ya ba da sanarwar cewar Koriyar za ta karfafa kera makaman nukiliya. A lokacin bikin bude taro Kim Jong Un ya kiyasta cewa shekarar ta 2023 da ke shirin kammala, ta kasance shekara mai girma na sauyi da manyan canje-canje, musamman ta fuskar karfin soja. A makwannin da suka gabata Koriyar ta Arewar, hanyar harba tauraron dan adam na farko na leken asiri na kasar,da gwajin harba makami mai linzami mafi karfi a tsakanin nahiyoyi.