1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Barazanar takunkumi kan Koriya ta Arewa

Ramatu Garba Baba
March 26, 2022

Amirka ta bukaci manyan kasashen duniya da su kakaba wa Koriya ta Arewa takunkumi mai tsauri a sakamakon kasasabar da Pyongyang tayi na harba makami mai linzami.

Nordkorea testet Interkontinentalrakete | Kim Jong Un
Shugaba Kim Jong Un na tafi bayan gwajin makaminHoto: KCNA/KNS/AP/picture alliance

Gwajin da Koriya ta Arewan ta gudanar a ranar Alhamis da ta gabata, ya kasance karo na farko da take harba makami mai karfin gaske tun bayan wanda tayi a shekarar 2017, matakin da ya matukar harzuka manyan kasashen na duniya tare da kiraye-kirayen a ladabtar da kasar. 

Kudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya haramta wa Koriya ta Arewa duk wani gwajin makami mai linzami da makaman nukiliya bayan baya ga sanya takunkumi kan shirye-shiryenta na kera makaman da aka ce nada hadarin gaske ga duniya baki daya.