Koriya ta Arewa na fuskantar yunwa
May 3, 2019Talla
Hukumar abinci ta duniya, ta ce karancin abincin a Koriya ta Arewa, na da nasaba ne da sauyin yanayi da ya haddasa fari da ambaliyar ruwa, sai kuma karancin man fetur da takin zamani da manoma suka fuskanta.
Wani bangaren matsalar kuwa ya hada har da takukuman da kasar ta gani, saboda neman tilasta wa Shugaba Kin Jong-Un, jingine nuna karfi da yake yi na mallakar makaman nukiliya.
Matsalar kuwa ta fi zafi ne a rayuwar kananan yara da mata masu shayarwa da ma wadanda ke dauke da juna biyu.