SiyasaJamus
Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami
September 15, 2021Talla
Sabon gwajin makami mai linzamin na zuwa ne a daidai lokacin da ministan harkokin wajen Chaina ya ziyarci birnin Seoul don tattaunawa kan gwajin makami mai cin dogon zangon da Pyongyang ta yi a baya-bayan nan. Jami'an tsaron gabar ruwan Japan na cewa makaman sun sauka ne wajen ruwan kasar. Idan aka tabbatar da gwajin na wannan Laraba a matsayin makami mai linzami, zai kasance makami na farko da Koriya ta Arewa ta harba tun watan Maris kuma hakan na nuni da ci gaba da take takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa kasar. Firanministan Japan Yoshihide Suga ya yi tir da harba makamin tare da bayyana shi a matsayin wuce gona da iri, ko kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.