Cacar baka tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu
March 7, 2016Koriya ta Arewa ta yi barazanar amfani da makamin nukiliya idan takwararta Koriya ta Kudu da Amirka suka yi atisayen sojoji da makamai a wannan Litinin kamar yadda suka tanada. Dakarun Amirka dubu 17 da na Koriya ta Kudu dubu 300 ne za su yi gwaje-gwajen makamai wanda suka ce ba a taba ganin irinsa ba, wata guda bayan gwajin makami mai cin dogon zango da Koriya ta Arewa ta yi.
Ita dai Koriya ta Arewa ta na daukar wannan atisaye a matsayin tsokanar fada. Da ma kasashen duniya sun kakaba mata wasu sababbin takunkumai na karya tattalin arziki bayan gwajin makaman da suka ce ta yi ba bisa ka'ida ba.
A lokacin da ya ke mayar da martani kan wannan batu, kakakin ma'aikatar tsaron Koriya ta Kudu Sang-Gyun ya gargadi gwamnatin Koriya ta Arewa da cewa:
"Dole Koriya ta Arewa ta yi watsi da akidar nan tata da ba ta amfana mata komai. Idan ko Koriya ta Arewa ta toshe kunnuwanta ta ki jin gargadin da muka yi mata, to sojojinmu za su mayar da martani ba tare da bata lokaci ba."