Koriya ta arewa ta gaiyaci supetoci tattaunawa game da batun rufe tasharta ta nukiliya
June 16, 2007Talla
Koriya ta arewa ta gaiyaci supetocin Majalisar Dinkin Duniya domin su tattauna batun rufe tasharta ta nukiliya.
Koriyan tace an kusa kawo karshen rikicin kudi tsakaninta da Amurka wanda ya janyo tsaiko ga rufe tashoshin nata.
Kanfanin dillancin labaru na Koriya ta arewan ya bada rahoton cewa,wakilin Koriya a hukumar ta IAEA Ri Je Son tuni ya aike da takardar gaiyata ga Muhammad El baradei shugaban hukumar.
Koriya ta arewan ta sha nanata cewa zata mutunta yarjejeniyar watan fabarairu na rufe tashoshinta nata na nukiliya da zarar ta karbi kudadenta dala miliyan 25 da Amurka dakatar a banki.