1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta gamu da sabon takunkumi

Suleiman Babayo
September 12, 2017

Ana ci gaba da martani kan sabon takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Koriya ta Arewa saboda gwajin makamin nukiliya kashi na shida da ta yi a ranar uku ga watan nan na Satumba.

New York UN Sicherheitsrat Nordkorea Sitzung
Babban zaman taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya saka takunkumi wa Koriya ta ArewaHoto: picture-alliance/Photoshot/L. Muzi

Wannan matakin takunkumin zai kawo karshen fita da kayayyakin atamfa daga Koriya ta Arewa zuwa kasashen ketere, da kuma zabtare man fetur da kasar ke bukata daga kasashen waje. Haka ya zama karo na tara da daukacin mambobin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke yarda da matakin takunkumi kan kasar Koriya ta Arewa tun daga shekara ta 2006 bisa kwaje-kwajen makamai masu linzami da na nukiliya. Tuni Geng Shuang mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China ya bayyana dalilan da ya saka gwamnatin China take goyon bayan sabon takunkumin:

China ta goyu bayan takunkumi kan Koriya ta Arewa

Geng Shuang mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ChinaHoto: picture-alliance/Kyodo

"China ta goyi bayan karin matakai da suka dace daga Majalisar Dinkin Duniya bisa martanin gwaji na shida na nukiya da Koriya ta Arewa ta yi. Muna fata mambobin Kwamitin Sulhu za su tabbatar da matsaya guda kan tura sako na hadin kai."

Masana'antun kayan tufafi ke matsayi na biyu wajen samar da kudaden shiga ga kasar Koriya ta Arewa daga musayen kudaden kasashen ketere. Sannan kudirin ya amince da katse sayar da wasu nauyin ma'adanan man fetur da aka sarrafa ga kasar Koriya ta Arewa, abin da galibi take samu daga kasar China. Tuni kasar Koriya ta Kudu ta nuna jin dadinta kan matakin na Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda Park Soo-Hyun mai magana da yawun shugaban kasra ke cewa:

Koriya ta Kudu ta gamsu da takunkumi kan makwabciyarta

Park Soo-Hyun mai magana da yawun shugaban kasar Koriya ta ArewaHoto: AP

"Muna nuna farin ciki da yadda daukacin mambobin Kwamtin Sulhu suka amince da matakin sabon takunkumi mai lambar kudiri 2375 kan Koriya ta Arewa cikin kankanin lokaci. Wannan kudiri da aka amince ya nuna kasashen duniya sun amince da matsanancin matakin takunkumi kan Koriya ta Arewa fiye da kudirin da ya gabata mai lamba 2371 bisa martani na gwajin nukiliya."

Karkashin tatunkumin ba a rufe asusun ajiya na Shugaba Kim Jong Un. A amince da kudirin ba tare da dakatar da shigar da daukacin man fetur zuwa kasar ba, da kuma rufe asusun ajiye na gwamnati da ke kasashen ketere ba. Firaminista Shinzo Abe na Japan ya ce ya dace a yi biyayya ga matakin na Majalisar Dinkin Duniya. Kasar China ce dai ke a matsayin babbar mai cinikayya da kasar Koriya ta Arewa.