Koriya ta Arewa ta harba rokoki uku
May 18, 2013Ofishin mai magana da yawun ma'aikatar tsaron ta Koriya ta Kudun ne ya tabbatar da wannan labarin inda ya kara da cewar Koriya ta Arewa ta harba makaman ne guda biyu da safe yayin da ta harba cikon na ukun da rana kuma an harba dukannin makaman ne daga gabar ruwa ta gabashin Koriya ta Arewan ne.
Mahukuntan Koriya ta Kudu da Japan wanda ke zaman doya da manja da Koriya ta Arewa sun ce makaman da aka harba ba su shiga kasashen su ba kuma sun ce ba su tantance ko harba makaman na da nasaba da atisiya na soji ba, sai dai Koriya ta Kudu ta ce ta na ci gaba da sanya idanu kan batun kuma ta na cikin shirin ko ta kwana.
Wannan dai shi ne karon farko da aka harba wani makami daga Koriya ta Arewa bayan aka kwashe tsawon lokaci ana samun tada jijiyar wuya tsakanin kasar da makotanta wato Japan da Koriya ta Kudu a watannin da su ka gabata dangane da batun makamin nukilya.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Halima Balaraba Abbas