Koriya ta Arewa ta harba sabon makami
October 22, 2025
Talla
Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta tabbatar da cewa makwabciyarta Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami mai cin dogon zango zuwa teku, ba tare da ta bayyana wani dalili ba.
Wannan lamari ya faru ne kwanaki kalilan kafin Koriya ta Kudu ta karbi bakuncin taron koli na ƙungiyar tattalin arzikin kasashen Asiya da Pasifik, wanda ake shirin gudanarwa a mako mai zuwa a birnin Gyeongju.
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugabannin kasashe da dama za su halarci taron, ciki har da Shugaba Donald Trump na Amurka da Xi Jinping na China.
Masana sun ce Koriya ta Arewa na iya yin wannan gwajin roka a matsayin wani nuni na karfin iko, ko kuma don jaddada matsayinta a idon duniya a matsayinta na ƙasa mai mallakar makaman nukiliya.