Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami
March 25, 2021Masana na ganin, wannan ba sabon abu bane, don kuwa kasar ta saba irin wannan gwajin a duk lokacin da aka nada sabon shugaba a Amirka, a matsayin jan hankali, ko watakila, a koma kan teburin sulhunta rikicin nukiliyar da ya sa Amirkan lafta mata takunkumi. Ba a dai san martanin da gwamnatin Shugaba Joe Biden za ta mayar kan gwajin ba, gwajin da a duk lokacin da aka yi shi, ke haifar da fargaba a zukatan gwamnatocin kasashen duniya, kan shirin nukiliyar Koriya ta Arewa, da ake zargin na tattare da hadura.
Amirka dai ta sanya wa Koriya ta Arewa takunkumi ne, bisa zarginta da tanadin kayan sarrafa makaman nukiliya, da gwajin sabbin makaman kare dangi da ta sake fasalta wa. Yunkurin sulhunta batun a tsakanin tsohuwar gwamnatin Donald Trump da Shugaba Kim Jong Un ya ci tura. Ana dai ci gaba da takaddama kan shirin nukiliyar Koriya ta Arewa da sauran manyan kasashen duniya.