Koriya ta Arewa ta mayar wa Amirka martani
April 15, 2017Talla
Choe Ryong Hae din ya bayyana haka ne a yayin wani paretin soji da dakarun Koriyar ta Arewan suka yi domin tunawa da cikon shekaru 105 da haihuwar jagoran Koriya Kim II Sung kakan shugaban kasar mai ci yanzu Kim Jong Un. Wannan furuci dai ya biyo bayan da Amirka ta aike da wasu manyan jiragen ruwa masu harba makamai masu linzami a sansanin sojinta da ke a Koriya ta Kudu saboda shirin ko ta kwana.