Koriya ta Arewa ta mika kai bori ya hau
September 19, 2005Yarjejeniyar ta kuma ce,kasar Amurka zata mutunta kasancewar Koriya ta Arewa a matsayin kasa mai yancin kanta,kuma ba zata kai mata hari ba,abinda Koriya ta Arewan take nanata tsoronta akai,wadda tace shi ya sanya ta fara shirinta na samarda makaman nukiliya.
Wannan sanarwa ita ta kawo karshen tattaunawar mako guda tsakanin kasashen Koriya biyu,Sin,Japan,Rasha da Amurka,wadanda suka tattauna har sau hudu tsakaninsu tun watan Agusta na 2003,tare da nufin shawo kan Koriya ta Arewa ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya.
Karkashin sabuwar yarjejeniyar,Koriya ta Arewa zata dakatar da dukkan shiryukanta na nukiliya,ta kuma koma ga yarjejeniyar hana yaduwar nukiliya,kana ta amincewa masu binciken nukiliya na kasa da kasa su sake binciken da suka fara.
Su kuma sauran kasashe a nasu bangare sun amince da bukatar Koriyan ta samun makamashi nukiliya da zata yi anfani da shi.
Hakazalika kasashen sun amince dage taron zuwa watan Nuwamba,yunkuri day a kare wani mataki da Amurka tayi niyyar dauka na kaiwa Koriya ta Arewa gaban komitin sulhu domin yiwuwar kafa mata takunkumi,batu da kasar Sin mai marawa Koriya baya bata goyon bayansa,wadda kuma Koriyan tace daidai yake da yaki akanta.
Tuni dai Amurka ta zargi Pyongyang da saba yarjejeniyar 1994,wadda karkashinta aka fara gina tashoshin nukiliya don samarda wutar lantarki,kodayake yarjejeniyar ta yau bata tabo wannan batu ba.
Amurka dai a halin yanzu ta nuna cewa tana bukatar fara lalata tashoshin nukiliya na Koriya ba tare da bata lokaci ba,yayinda Koriyan tace tana so ne a tsarin daki daki.
Amurkan ta kuma sassauto ta amince cikin yarjejeniyar ta yau,ta maida hulda sannu a hankali tsakaninta da gwamnatin Kim Jong il.
Koriya ta Arewan kamar yadda hukumomin agaji suka ruwaito ta fuskanci karancin abinci hakazalika tana matukar bukatar makamashi domin hasken wutar lantarki da take samarwa a yanzu bai ko kusa isa biyan bukatar lantarki na kasar ba.
Karkashin yarjejeniyar kuma,sauran kasashe biyar sun baiyana aniyarsu ta taimakawa Koriya ta Arewan da makamashi,ita kuma Koriya ta Kudu tace a shirye take ta samarwa Koriya ta Arewa wutar lantarki mai karfin kilowatt miliyan biyu.
Takaddama akan batun nukiliya na Koriya ta Arewa ya fara ne a lokacinda Amurka ta zargi Koriyan da kokarin kera makaman nukiliya a asirce tana mai saba yarjejeniyar 1994.
Koriya ta Arewan a nata bangare ta fatattaki masu binciken nukiliya na kasa da kasa hakazalika tace ta cimma nasarar kera makamin kare dangi.
Shugaba Bush na Amurka dai tun farko ya jera sunan Koriya ta Arewa cikin kasashe kamar Iran da Irak a lokacin mulkin Saddam Hussein da cewa kasashen yan taadda ne su.Ita kuma Koriyan ta hakikance cewa ci gaba ba zai samu ba har sai Amurka ta sauya manufofinta.