1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nuna makami mai cin dogon zango

Abdoulaye Mamane Amadou
October 10, 2020

A yayin wani faretin soja da aka yi Koriya ta Arewa ta nuna wani sabon makami mai linzami da ke cin dogon zango wanda masana suka cewa shi ne irinsa na farko mafi girma.

Südkorea | TV-Übertragung Nordkorea | 75. Gründungstag der Arbeiterpartei
Hoto: Jung Yeon-Je/AFP/Getty Images

Koriya ta Arewa ta sake nuna wani sabon makami mai linzami da ka iya cin dogon zango a yayin wani faretin sojan da aka yi a birnin  Pyongyang.

An hango motocin soja dankare da sabon makamin mai suna ICBM a yayin faretin, kana masana da kungiyoyin fafatukar yaki da makami masu linzami na cewa sabon makamin da ke zama irinsa na farko mafi girma a duniya da kan iya keta nahiyoyi.