Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami
September 3, 2017Dakarun sojan Koriya ta Kudu sun bayyana cewa suna da yakini cewa Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamin nukiliya da ke zama a karo na shida bayan da ta fahimci an samu girgizar kasar da karfinta ya kai maki 6.3. Wannan kuwa na zuwa ne bayan da mahukuntan na birnin Pyongyang suka yi ikirari na cewa shugaban kasar ya kai ziyarar gani da ido na makamin (Hydrogen Bom) da ke zama sabon makami da zai iya kaiwa a harba daga wata nahiya zuwa wata.
Koriya ta Arewa dai ta yi jawabi da misalin 06:30 agogon GMT, yayin da daga bangaren Koriya ta Kudu shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokokin kasar ya ce a za ta iya yiwuwa Koriya ta Arewa ta yi gwaji ne na makami da ke zama niniki hudu ko biyar na irin makamin da aka kai hari a yankin Nagaski na Japan a shekarar 1945.
A shekarar bara ne dai a watan Satimba Koriya ta Arewa ta yi gwaji na irin wannan makami da ke zama gwaji karo na biyar, wannan dai na nuna irin kokarin da Koriya ta Arewa ke yi na ganin ta dangana da mallakar makamin nukiliya da za ta iya harba shi har zuwa tsakiyar Amirka.