1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta sake jaddada goyon baya ga Rasha

November 30, 2024

Koriya ta Arewa ta sake tabbatar wa kasar Rasha da ci gaba da samun cikakken goyon bayanta a yakin da take yi da kasar Ukraine.

Shugaba Kim da Putin a wata ziyara a Rasha
Shugaba Kim da Putin a RashaHoto: Yonhap/picture alliance

Shugaban Koriya ta Arewan Kim Jong Un ne ya shaida wa ministan tsaron Rasha Andrei Belousov hakan a birnin Pyongyang, kamar yadda kafofin watsa labaran Koriyar suka tabbatar a yau.

Kafofin dai sun ambato Shugaba Kim na fadin kasashen yammacin duniya karkashin jagorancin Amurka sun saka Ukraine yin amfani da makamai masu cin dogon zango wajen far wa yankunan Rasha.

Kididdiga dai ya nunar da cewa kasashen Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa da ma Amurka, na da sojoji sama da dubu goma da suka aika Rasha, inda wasu daga cikin su ke a yankin Kursk da ke a hannun Ukraine, inda take maida martani ga Rasha.

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya yi gargadin cewa sojojin Koriya ta Arewa na iya haura dubu 100 wadanda ke goyon bayan Rasha.