1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya Ta Arewa ta sanar da rufe tashar nukiliya ta Yongbyon

July 15, 2007

Sifetocin MDD na shirin tabbatar da sanarwar da KTA ta bayar cewa ta rufe tashar nukiliya ta Yongbyon. Tun a jiya asabar dai jami´an na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA suka isa kasar ta KTA don sa ido akan aikin rufe tashar nukiliyar. Shugaban hukumar Mohammed El-Baradei ya yi fatan kammala aikin salim alim.

El-Baradei:

“Ina sa rai wannan aiki zai gudana cikin tsanaki kamar yadda muka amince a cikin yarjejeniyar da muka kulla.”

Shi kuwa wakilin Amirka Christopher Hill ya yi maraba da sanarwar ta gwamnatin Pyongyang ya na mai cewa shi ne matakin farko na kwance damarar kasar ta KTA. Ma´aikatar harkokin wajen Amirka ta ce tana sa ran ganin an dauki mataki na gaba inda ake tsammani KTA zata bayyana dukkan shirye shiryenta na nukiliya tare da lalata wadanda ta ke amfani da su yanzu. Rasha da sauran kasashen duniya sun yi maraba da rufen tashar nukiliyar ta Yongbyon.