1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKoriya ta Kudu

Koriya ta Arewa ta soki Amurka kan nukiliya

November 18, 2025

Pyongyang fadar mulkin Koriya ta Arewa ta ce yarjejeniyar kera makamin nukiliya na karkashin teku daka kulla tsakanin Amurka da Koriya ta kudu zai kara dagula tsaro a yankin

Yarjejeniya Makamin nukiliya tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu
Yarjejeniya Makamin nukiliya tsakanin Amurka da Koriya ta KuduHoto: Gang Duck-chul/Yonhap/AP

Koriya ta Arewa ta ce yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Koriya ta Kudu da Amurka na samar da makamin nukiliya na karkashin teku ba zai haifar da komai ba illa kara tashin hankali a yankin.

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Lee Jae Myung ya sanar da hakan a wata yarjejeniyar tsaro da Kasuwanci da suka kulla da Washington, da suka kunshi shawarwari na ci gaba da habaka jiragen ruwa masu aiki da makamashin Nukiliya.

Seoul ta ce ta samu goyon baya don fadada ikonta akan habaka Uranium da sake sarrafa man Fetur