Koriya Ta Arewa ta soki lamirin jakadan Amirka a Koriya Ta Kudu
December 10, 2005Talla
KTA ta yi Allah wadai da jakadan Amirka a birnin Seoul na KTK dangane da kwatanta kasar mai bin tsarin kwaminisanci da cewa haramtacciyar gwamnati ce mai aikata laifi. Gwamnati a birnin Pyongyang ta ce furucin da jakadan yayi tamkar kaddamar da yaki ne wanda ya dagargaza tattaunawar da ake yi akan makaman nukiliya. A wajen wani taro da ya halarta jakadan Amirka a KTK Alexander Vershbow ya ce gwamnatin birnin Pyongayang na tafiyar da wata harkar sayar da makamai da miyagun kwayoyi, saboda haka gwamnatin Washington ba zata dage takunkuman da ta dora mata ba matukan tana ci gaba da aikta wannan aikin haramun.