Koriya ta Arewa ta soki manufar taimaka wa Ukraine
January 27, 2023A daidai lokacin da rahotannin ke cewa Rasha na kara zafafa hare-haren da ta ke kai wa a arewa da gabashin Ukraine, ita kuwa Koriya ta Arewa ta soki matakin Amirka na taimaka wa gwamnatin Kyiv da tankunan yaki da ta ce, taimakon ba zai yi tasiri ba illa ya kara rura wutar rikicin yakin da ke ci a gabashin Turai.
Kalaman na kanwar Shugaba Kim Jong Un, wato Kim Yo Jong, sun tabbatar da zargin da aka jima ana yi wa Koriya ta Arewa na mara wa Rasha baya a mamayar Ukraine, dama wannan ba shi bane karon farko da kasar ke sukar Amirka da zama kanwa uwar gami a rikicin makwabtan biyu.
A daya bangaren, kasashen tarayyar Turai sun dauki mataki na tsawaita takunkumin karya tattalin arzikin da suka sanya wa Rasha da wasu karin watanni shida a taron da suka yi a wannan Jummar, takunkuman sun hadar da tazgaro ga hada-hadar mai da musayar kudade da wasu haramcin da suka shafi Shugaba Vladimir Putin kai tsaye.