Koriya ta Arewa ta soki takunkumin da aka sa mata
December 24, 2017Koriya ta Arewa ta mayar da martani ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya biyo bayan takunkumi da aka kakaba wa kasar saboda gwaje-gwajen da take yi na makamai masu linzami, inda ta bayyana matakin da aka dauka a kanta a matsayin yunkurin "yin yaki da ita".
Wannan dai shi ne martani na farko daga bangaren na mahukuntan birnin Pyongyang da ke zuwa bayan kwamitin sulhun na MDD ya amince da kudirin da Amirka ta gabatar masa kan kakaba wa Koriyar ta Arewan, sabon takunkumi da zai hana wa kasar samun wadataccen man fetur da ke zama muhimmi kan lamuranta na yau da kullum, dama yunkurin maido da 'yan kasar da ke aiki a kasashen waje kasar na amfana. Shi dai wannan takunkumi ya samu goyon bayan kasashe ciki har da kawar Koriya ta Arewan wato China.