Kim Jong Un ya cilla makami mai linazami
January 15, 2022Talla
Sabbin gwajin makamai masu linzamin da Pyanyong ta yi, na zuwa ne sao'i kalilan bayan gargadin da ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewar ta yi , na daukar mataki masu zafi kan gwamnatin Joe Biden idan ba ta sassauta takunkuman da ta sa ba.
Sai dai masana na ganin rashin jituwa tsakanin manyan kasashen biyu, na cigba da haifar da barazana ga zamantakewa a yankin Koriya kamar yadda Farfesa Yang Moo-jin na jami'ar Koriya ta Arewa yake cewa "Wannan sabon gwajin, sako ne Koriya ta Arewa ke isarwa, cewa ba za ta yi watsi da aikinta na makamai masu linzami ba. Kuma martani ne na dakile takunkuman da Amirka ta sa mata, sai dai ramuwar gayyar da kasashen buiyu ke wa juna, ba abin da ke haifarwa sai tashin hankali a yankunan Koriya."