Koriya ta arewa ta yi barazanar yin wasu gwajin makamai
July 7, 2006ƙasar Koriya ta arewa ta baiyana a yau cewa gwajin makamai masu linzami da ta yi ba hari ne ta kai a kan wani ba, a saboda haka ta ce babu wata hujja da zaá nemi a tsamgwame ta. A yau ɗin kuma jakadan Amurka Christopher Hills ya isa yankin na Asia domin ƙarfafa matsayin Amurka cewa wajibi ne a jawo hankalin Pyongyang domin ta shiga taitayin ta. Amurkan dai ta gaza samun goyon baya a yunkurin ganin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya zartar da ƙudiri a kan koriya ta arewa bisa gwajin makaman masu linzami. ƙasashen Rasha da China sun soki lamirin yin tofin Allah tsine ga koriya ta arewa a maimakon hakan sun bukaci a yi mata jan kunne ne kawai. Koriya ta arewan ta yi barazanar cewa idan aka matsa mata tana iya yin gwajin wasu makaman a nan gaba. Shugaban Amurka George W Bush ya ce wajibi ne kasashen duniya su dauki mataki na bai daya a kan ƙasar Koriya ta arewa wadda yace tana wuce gona da iri. A nasa ɓangaren shugaban ƙasar Sin Hu Jintao ya shaidawa shugaban na Amurka cewa ƙasar Sin bata goyon bayan dukkan wani abu da zai kawo rashin kwanciyar hankali a yankin.