Koriya ta Arewa ta yi gwajin sabon makami
October 19, 2021Talla
Wannan sabon gwajin na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da Amirka ta sake tabbatar da aniyarta ta komawa kan teburi domin ci gaba da tattaunawa kan makaman da Koriya ta Arewa ta mallaka, da ma yadda a baya-bayan nan take ci gaba da gwaje-gwajen sabbi da ake gani na zama barazana.
Dakarun koriya ta Kudu da na Amirka na ci gaba da kula da yadda makaman ke tashi, kuma sun tabbatar da wannan ya taso ne daga tashar ruwan Sinpo da ke gabashin kasar.
Firaministan kasar Japan Fumio Kishidi ya yi tir da Allah wadai da wanna gwajin da Koriya ta Arewa ke ci gaba da yi. Ita dai Koriya ta Arewa tana wannan gwaje-gwajen ne domin nuna karfin makamanta, matakin da ya yi hannun riga da sharuddan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.