Koriya ta Arewa ta yi sabon gwajin makami
November 29, 2017Koriya ta ce ta cika burin nata tunda ta samu makamin da zai iya kaiwa ga dukannin jihohin Amirka. Sai dai da yake mayar da maratani kan wannan sabon gwajin shugaban Amirka Donald Trump da ya kammala wani dogon rangadi a yankin na Asiya, ya ce za su dauki mataki.
"Yadda kuma kuka ji, kuma yadda wasu daga ciki suka sanar, lalle Koriya ta Arewa ta yi sabon gwaji na makami mai cin dogon zongo. Abun kawai da zan ce shi ne za mu dauki mataki a kanta. A yanzu haka ina tare da Janar Matiss shugaban ma'aikatar tsaro, kuma mun yi doguwar tattaunawa da shi kan wannan batu. Don haka za mu dauki mataki a kai."
Kasar Japan ta ce wannan sabon gwaji wata tsokala ce da ba za a yarda da ita ba, sannan kuma Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa domin duba wannan lamari na sabon gwajin makamin da Kiriya ta Arewa ta yi bayan shiru da ta yi na wajen watanni biyu ba tare da gwajin ba.