Koriya ta Arewa ta yi wa Amirka gargadi
April 23, 2017Talla
Barazanar Koriya ta Arewa na wannan Lahadi, na zuwa ne daidai lokacin da wasu jiragen ruwa na kasar Japan biyu ke wani atisaye da jiragen yakin Amirka a yankin yammacin Pacific. Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin wasu manyan jiragen kasar su keta gabar ruwan yankin na Koriya, a martaninta kan yunkurin Koriya ta Arewa na gwada makaman nukiliya da masu linzami.
Ba a dai bayyana takamaiman wuraren da Amirkar ke hari ba a yankin, sai dai kalaman mataimakin shugaban Amirka a jiya Asabar na cewa nan ba da jimawa ba ne jiragen za su isa.
Koriya ta Arewar ta kuma kama wani dan kasar Amirka da ke kokarin ficewa daga kasar a wannan Lahadin, bayan kasancewar wasu Amirkawan biyu da ke tsare tun farko.