Dangantaka ta yi tsami tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu
June 10, 2024Talla
Dangantakarda ke tsakanin Koriyar ta arewa da ta kudu, ta yi tsami fiye da goman shekaru. A makwannin baya-bayan nan, Pyongyang ta aike da daruruwan balan- balo cike da shara a wani abin da ta kira kashedi wa Koriya ta Kudun saboda farfagandar da take yi na kasashen yammacin duniya.