Koriya ta arewa tace a shiye take ta bar shirinta na nukiliya
October 10, 2006Talla
Wani jamiin Koriya ta arewa yace gwamnatin Pyongyang a shirye take ta koma teburin tattaunawa na kasa da kasa akan makamanta,tare kuma da barin shirinta na kera makamin atom muddin dai Amurka ta dauki matakai da suka dace.
Kanfanin dillancin labaari na Koriyan Yonhap ya ruwaito ta bakin jamiin cewa,wannan gwaji yana nufin baiyana aniyarsu ce ta neman zaunawa kan teburin shawarwari da kasar Amurkan.