1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa za ta bada hadin kai ga binciken nukiliya

February 29, 2012

Hukumomin Pyong Yang sun amince komawa tebrin shawara da gamayyar kasa da kasa game da takkadamar nukiliya

This image from television shows the demolition of the 60-foot-tall cooling tower at its main reactor complex in Yongbyon North Korea Friday June 27, 2008. North Korea destroyed the most visible symbol of its nuclear weapons program Friday in a sign of its commitment to stop making plutonium for atomic bombs. (ddp images/AP Photo/APTN)
Tashar nukiliyar YongbyonHoto: ddp/AP/APTN

A wata sanarwa da ta fiddo yau, gwamnatin Amurika ta ce Koriya ta Arewa ta amince ta bada hadin kai ga kokarin warware rikicin nukiliya.

An cimma wannan matsayi, a wata tattanawar da ta hada hukumomin Pyong Yang da na tawagar Amurika a kasar China.Koriya ta Arewa, ta yi alkawarin buda tashoshinta na sarrafa makamashin nukiliya ga masu bincike na kasa da kasa, sannan kuma ta koma tebrin shawara tare da sauran kasashe biyar da ke kokarin warware matsalar cikin ruwan sanhi.

A daya wajen, Amurika ta yi alkawarin bada tallafin abinci ga al'umar kasar dake fama da matsalar yinwa.

Tun shekara 2009 ne Pyong Yang ta kori sipetocin Hukumar yaki da yaduwar makaman nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA, wanda suka kaddamar da bincike a tasharta ta samar da makamashin nukiliya dake Yongbyon.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Usman Shehu Usman