1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa za ta daina gwajin makamai

April 29, 2018

Kasar Koriya ta Arewa za ta rufe cibiyar nan ta gwaje-gwajen makaman Nukiliya a kasarsa, cikin watan gobe na Mayu mai shirin kamawa.

Nordkorea  Kim Jong Un
Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa tare da manyan hafsoshin kasarsaHoto: picture alliance/dpa/AP Photo/Korean Central News Agency

Shugaba Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa, ya ce zai rufe cibiyar nan ta gwaje-gwajen makaman Nukiliya a kasarsa, cikin watan gobe na Mayu mai shirin kamawa. Mr. Kim wanda ya fadi hakan a ziyararsa ta tarihi a kasar Koriya ta Kudu, ya yi alkawarin gayyatar kwararru daga Amirka da Koriya ta Kudu da 'yan jarida don ganin yanda za a rufe cibiyar.

Yayin ziyarar ta Juma'a dai, shugabannin Koriyoyin biyu, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar daina amfani da makaman Nukiliya a yankin nasu, abin kuma da zai kawo karshen gardama tsakaninsu. Tun cikin shekarun 1950 ne dai ake ta ja-in-ja tsakanin Koriyoyin biyu, ba tare da wani shiri na sulhu a tsakani ba.

Wasu masana kimiyya 'yan kasar China dai sun ce cibiyar ta lalace, a gwajin baya-bayan nan da Koriya ta Arewar ta yi, sai dai fa wasu jami'an leken asirin Amirka sun ce wajen na aiki.