Kim na shirin sulhu da Koriya ta Kudu
September 30, 2021Talla
A watan Agusta ne gwamnatin Pyongyang ta yanke layin sadarwa tsakaninta da Koriya ta Kudu, bayan atisayen soji na hadin gwiwa tsakanin Koriya ta Kudu da kasar Amirka.
Ana dai ganin Koriya ta Arewa na shirin sabunta hulda da makociyarta ta Koriya ta Kudu don samun sassaucin karayar tattalin arziki sakamakon takunkumin Amirka da sauran kasashen duniya.