1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta sake harba makamin roka

Abdourahamane Hassane
July 19, 2023

Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami masu cin gajeren zango guda biyu. Wadanda suka ci tafiyar kilomita 550 kafin su fada cikin tekun Japan.

Atomgetriebenes U-Boot USS Kentucky trifft in Südkorea ein
Hoto: YONHAPNEWS AGENCY/picture alliance

Sakamakon karuwar takun saka da Koriya ta Arewa, Amurka da kawayenta da Koriya ta Kudu sun amince a watan Afrilu da ya gabata  don karfafa hadin gwiwar soji. Wanda kasashen suka amince da  jibge jirgin ruwa mai dauke da makaman kare dangi a tekun. Abin da ya kara fusata Koriya ta Arewan.