Koriya ta harba makami mai linzami
January 30, 2022Makamin mai linzamin wanda Koriya ta harba daga Jagang inda ta saba harbawa da ke a gabar tekun gabashin kasar, ya yi gudun kilomita 800 a cikin mitoci 30 daga wurin da aka harbashi a tafiyar kololuwa ta kilomita dubu biyu kafin ya fada a cikin tekun Japan. A cikin wata sanarwa da ya bayyana shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae In ya ce Koriya ta Arewa na nesa da yin amana a kan bukatar kasashen duniya na yin watsi da gwaje-gwajen na makaman nukilya kafin ya bayana kiran taron gaggawa na tsaro na kasarsa. Wannan gwaji wanda shi ne na bakwai tun farkon wannan shekara na zuwa ne a daidai lokacin da China kawarta ke shirin karbar bakwancin wasannin Olympic na sanhi hunturu, yayin da Koriya ta Kudu za ta gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Maris da ke tafe.