SiyasaAsiya
Kim ya gabatar da makami mai linzami da ke cin dogon zango
October 11, 2025
Talla
Gwamnatin Koriya ta Arewa ta kaddamar da sabbin makaman ne a wajen faretin sojoji a ci gaba da bikin murnar cika shekaru 80 da kafuwar jam'iyyar Ma'aikata ta kasar wato "Workers' Party of Korea (WPK)", inda Shugaba Kim ya nuna wa duniya karfin sojin da kasar ke da shi da kuma diflomasiyya tsakanin Koriya da kawayenta.
Karin bayani:Kim ya nufi China domin halartar bikin atisayen sojoji
Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai Firimiyan China Li Qiang da tawagar Rasha karkashin jagorancin Tsohon Shugaban Kasar Dmitry Medvedev da kuma Shugaban Jam'iyyar Kwamunisanci na Vietnam To Lam.