1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar da ke mulki a Koriya ta sha kaye a zaben majalisa

Abdourahamane Hassane
April 11, 2024

Jam'iyyar ‘yan mazan jiya ta shugaba Yoon Suk Yeol na Koriya ta kudu, ta sha mummunar kaye a zaben 'yan majalisar dokoki daga hannu jam'iyyar masu ra'ayi kawo sauyi inda ta rasa rinjaye a majalisar.

Hoto: Jeon Heon-Kyun/AP/picture alliance

 Kafofin yada labaran kasar sun ce shugaba Yoon, na jam'iyyar PPP da ke yin mulki, wanda aka zaba a shekara ta 2022,ya zama shugaban kasar Koriya ta Kudu na farko da jam'iyyarsa ta rasa rinjaye a majalisar dokokin. Masu aiko da rahotannin sun ce shugaban jami'yyar ta masu ra'ayin rikau,zai gamu da babban cikas wajen aiwatar da manufofinsa a tsawon wa'adin mulkinsa,wajen aiwatar da dokoki da kasafin kudi saboda   rashin rinjayen.