1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKoriya ta Kudu

Koriya ta Kudu: Kotu ta ba da belin Yoon Suk Yeol

March 7, 2025

An saki tsigeggen shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol daga gidan yari bisa umurnin wata kutu da ke birnin Seoul fadar gwamnati.

Kotu ta ba da belin Yoon Suk Yeol
Kotu ta ba da belin Yoon Suk YeolHoto: Joen Heon-Kyun/AP Photo/picture alliance

Kotun birnin Seoul ta amince da bukatar da lauyoyin Yool Suk Yeol suka shigar a gabanta kan soke sammanci kama shi, inda ta ba da belin tsigeggen shugaban a wannan rana ta Juma'a, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar na Yonhap ya ruwaito.

Kotun ta ce ta dauki wannan mataki na sakin Yoon domin tabbatar da haske da kuma kore duk wani shakku a game da binciken da take gudanarwa kan tuhume-tuhume da aka mika mata a kan shugaban da aka tsare tun ranar  26 ga watan Janairun 2025.

Karin bayani: Shugaba Yoon ya ki bayar da kai bori ya hau— Masu bincike

A halin yanzu dai Yoon Suk Yeol na a matsayin shugaban da aka dakatar bayan da majalisar dokoki da kada kuri'ar tsige shi, domin hukuncin karshe na a hannun kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudu, wadda ake jira ta tabbatar ko shin matakinsa na kafa dokar soji a karshen shekarar bara ya sabawa dokokin kasar.