1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Koriya ta Kudu za ta tallafa wa takwararta

Ramatu Garba Baba
August 15, 2022

Koriya ta Kudu ta shirya tallafa wa makwabciyarta Koriya ta Arewa ta fuskar inganta tattalin arzikinta muddun za ta amince ta yi watsi da shirin nukiliyarta.

Südkorea Präsident Yoon Suk-yeol
Hoto: Ahn Young-joon/AFP

Koriya ta Kudu ta yi alkawarin tallafa wa Koriya ta Arewa inganta tattalin arzikinta muddun ta amince ta yi watsi da shirinta na kera makaman nukiliya da ake wa kallon mai hadarin gaske. Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol ne ya sanar da hakan a wannan Litinin a yayin da ya ke jawabi a bikin tuna ranar da yankin ya samu 'yancin kai daga kasar Japan. 

Shugaba Yoon ya ce, a shirye ya ke, ya taimaka ma makwabciyarsa ta hanyar inganta harkar noma da asibitoci dama sauran abubuwan more rayuwa muddun ta amince da tayin.

Kawo yanzu, Koriya ta Arewa da a baya ta sha gargadin makwabciyartata da Amirka kan su guji haddasa munmunan tashin hankali na tsaro a sakamakon atisayen sojoji na hadin gwiwa da suke yi, ba ta mayar da martani ba.

Amma hankalin manyan kasashen duniya ya karkata yanzu kan sabuwar dangantaka a tsakanin Koriya ta Arewa da Rasha, inda kafafen yada labaran Koriya ta Arewa ke ta sharhi kan wata tattaunawa da aka yi a tsakanin Shugaba Vladimir Putin da takwaransa Kim Jong-un.