1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake dawo da sufuri a kasashen Koriya

Gazali Abdou Tasawa
December 26, 2018

Kasashen Koriya ta Arewa da ta Kudu sun gudanar da bikin sake bude hanyoyin sufurin jiragen kasa da na motoci tsakaninsu, shekaru 70 bayan rufe su.

Südkorea schickt Zug nach Nordkorea (picture alliance/dpa/Pool Reuters/K. Hong-Ji)
Hoto: picture-alliance/dpa/Pool Reuters/K. Hong-Ji

Wannan dai na zaman wani mataki na neman inganta huldarsu duk kuwa da cikas din da tattaunawar da kasashen biyu ke yi kan batun makaman nukiliya ke fuskanta. Tun da sanyin safiyar wannan Laraba wani ayarin jami'an gwamnatin Koriya ta Kudu  a cikin wani jirgin kasa mai dauke da motoci tara ya ketara zuwa Koriya ta Arewa domin halartar bikin, wanda zai wakana a tashar jiragen kasa ta Paumun a yankin Kaesong. 

A shekara ta 1948 ne dai kasashen biyu suka katse hanyoyin jiragen kasa da na motoci a tsakaninsu. Yanzu haka Koriya ta Kudu ta sanar da ware kudi sama da Dalar Amirka miliyan 56 domin gudanar da aikin sabunta hanyoyin jiragen kasan a shekaru biyar masu zuwa.