1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotin Kolin Najeriya ta halata zaben Goodluck Jonathan

December 28, 2011

A zaman da ta yi a birnin Abuja Kotin Kolin Najeriya ta yi fatali da karar da CPC ta shigar na yin watsi da zaben shugaban kasa.

Goodluck Jonathan shugaban kasar Najeriya
Shugaban kasar Najeriya Goodluck JonathanHoto: AP

A wani zaman da ta yi a birnin Abuja,Kotin kolin Najeriya, ta tabbatar da hallacin zaben shugaban kasa Goodluck Jonathan.Kotun ta yi fatali da karan da babbar jam'iyar adawa ta CPC ta shigar ,inda ta bukaci a yi watsi da sakamakon zaben, wanda ta ce an tafka magudi a cikin sa.

A yayin da yake maida martani game da sakamakon,dan takara jam'iyar CPC janar Mahamadu Buhari mai ritaya cewa yayi:

"Duk mutumen da ya shaidi yadda zaben ya gudana, zai tabbatar da cewar hukuncin da kotin koli ta yanke siyasa ce kawai, ba ayi dogaro da hujjojin shari'a ba.Kuma hakan bai bamu mamaki ba, cemma mun san a rina,mun san da zata bi sahun kotunan da su ka yanke hukunci a kararakin da mu ka shigar na shekarun baya."

Wannan sakamako da kotun koli ta bada, ya zo a daidai lokacin da Najeriya ta shiga wani hali na tsaka mai wuya, sanadiyar hare-haren bama bamai da suka zama ruwan dare.

Hatta a ranae Talata,rahotani daga jihar Delta, sun ce bam ta tarwatse a cikin wata makarantar islamiya inda yara bakwai suka ji raunuka.

Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu