Kotu a Bamako ta daure dan jarida da ya ba da labarin Tiani
March 23, 2026
Talla
Kotu a birnin Bamako ta yanke wa dan jaridar Mali, Youssouf Sissoko, hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.
Hukuncin ya biyo bayan jaridarsa ta L'Alternance, da ta buga labarin da ke sukar shugaban gwamnatin mulkin soja na Nijar, Abdourahamane Tiani, kan zargin da ya yi wa Faransa da Côte d'Ivoire da Benin; da hannu a harin filin jirgin sama na birnin Yamai, wanda daga bisani kungiyar IS ta dauki alhaki.
An tuhume Sissoko ne da yada bayanan karya da b'ata suna ga gwamnati da cin zarafi ga shugaban kasar waje.
Kungiyoyin ‘yan jarida a Mali sun ce hukuncin ya nuna koma-baya ga ‘yancin aikin jarida.
Mali da Nijar da Burkina Faso da duk ke karkashin rundunonin soja, na ci gaba da fuskantar suka kan takaita ‘yancin jama'a da na aikin jarida.