Kotu a Kenya ta ci tarar manyan jami'ai
March 29, 2018Talla
Fitattcen dan siyasa na jam'iyyar adawa ta NASA Miguna Miguna, ya mamaye kafofin yada labaru ne bayan korarsa daga Kenyan da aka yi a karon farko a watan daya gabata, kana yunkurin sake dawowarsa kasar a wannan makon, ya tayar da rikicin siyasa.
A dai dai lokacin da jami'an hukumar shige da fice ke tsare da Miguna na tsawon kwanaki biyu a filin jiragen saman Nairobi, sau biyu babbar kotun Kenyan ta umurci ministan cikin gida Fred Matiangi da shugaban hukumar 'yan sanda Joseph Boinnet da manyan jami'an shige da ficen kasar, da su sakeshi.
A kan haka ne alkalin kotun George Odunga ya ci tarar kowanensu dalar Amurka dubu biyu, saboda sabawa kundin tsarin mulkin kasa ta hanyar kin bin umurnin kotu.