Masar ta rataye mutanen da suka kashe 'yan sanda
April 26, 2021Talla
Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutane tara da ake zargi 'yan kungiyar IS ne da suka kashe jamai'an tsaro 14 a ofishin 'yan sanda a shekarar 2013 a wajen birnin Alkahira.
Hukuncin kisan ya fuskancir zazzafar adawa daga kungiyoyin kare hakkin bil Adama, wadanda ke cewa Masar ta kashe mutane sama da 100 a shekarar 2020 kadai, adadin da ya ninka hukuncin da take yi har sau uku a cikin shekara daya.